Ma’aikatar Ilimi ta Nijeriya ta bayyana cewa ɗaliban sakandare a fannin “Art” ba za a sake tilasta musu samun kiredit a lissafi ba a jarabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO a matsayin sharadin samun gurbin karatu a jami’a ko kwalejin fasaha.
Tsarin da aka saba da shi na bukatar samun akalla kiredit biyar ciki har da Turanci da Lissafi ya kasance yana shafar dukkan bangarorin karatu wanda ya hada da ilimi, zamantakewa, da fasaha. Amma sabon tsarin ya bayyana cewa, lissafi ya zama tilas ne kawai ga waɗanda ke neman karatu a fannoni na kimiyya, fasaha da zamantakewa.
Jaridar Punch ta ruwaito sabbin ka’idojin da aka sabunta na shiga jami’o’i da kwalejojin fasaha, ɗalibai su sami akalla kiredit biyar a fannonin da suka dace ciki har da Turanci, akalla a zama biyu kacal. Lissafi na wajibi ne kawai ga fannonin kimiyya, fasaha, da zamantakewa.
Ga masu neman gurbi a Poly kuwa, kiredit huɗu ciki har da Turanci ga fannoni marasa kimiyya, da kuma lissafi ga fannoni masu nasaba da kimiyya.
Ma’aikatar ta ce sabon tsarin na nufin rage cikas ga ɗalibai yayin da ake ci-gaba da kiyaye ingancin ilimi, kuma ya shafi dukkan jami’o’i, kwalejojin ilimi, kwalejojin fasaha, da cibiyoyin koyon sana’o’i a fadin ƙasar.