Wani likita mai suna Dr. Michael Ajidahun, wanda aka fi sani da “The Bearded Dr. Sina” a X, ya bayyana cewa maza kan fuskanci alamomin juna biyu yayin da matansu ke ɗauke da ciki, abin da ake kira “Couvade Syndrome”.
A cewarsa, wasu maza kan fara jin amai, ƙarin nauyi, da sauyin yanayi kamar mata masu ciki, inda wasu ma sukan ji ciwon ciki da gajiya sosai kamar yadda Punch ta ruwaito.
Masana sun bayyana cewa Couvade Syndrome yanayi ne na kwakwalwa da jiki inda miji ke nuna alamomin juna biyu saboda sauyin hormone ko damuwar da ke tattare da ciki.
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta bayan wani mutum ya koka cewa babu wanda ya damu da lafiyarsa bayan matarsa ta haihu, abin da ya tayar da tattaunawa kan kula da lafiyar kwakwalwar maza bayan haihuwa.