Mahaifin marigayi Bilyaminu Bello, Alhaji Ahmed Bello Isa, ya bayyana cewa ya karɓi afuwar da Shugaba Bola Tinubu ya bai wa surukarsa, Maryam Sanda, yana mai cewa tun da dadewa ya yafe mata bisa kisan ɗansa da ta yi.
A yayin taron manema labarai an Abuja, Alhaji Bello ya ce afuwar shugaba Tinubu “nufin Allah ce,” wacce za ta bai wa Maryam damar kula da ’ya’yanta biyu.
Haka kuma ya ce a matsayinsu na Musulmai, sun amince da duk abin da Allah Ya kaddara, yana mai jaddada cewa “ramuwar gayya ba za ta dawo da Biliyaminu ba, amma yafiya na kawo salama.”
Maryam Sanda, ’yar tsohuwar ma’aikaciyar Aso Savings, an yanke mata hukuncin kisa a watan Janairu 2020 bayan samun ta da laifin kisan mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan uwan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Bello Haliru Mohammed.
Lamarin da ya faru a watan Nuwamba 2017 an Abuja ya tayar da ƙura a fadin ƙasar kan matsalar tashin hankali tsakanin ma’aurata da batun adalci.
Alhaji Bello ya bayyana cewa tun kafin kotu ta yanke hukunci a 2019, ya riga ya roƙi gwamnati ta yi Maryam Sanda afuwa kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.