Shugaban hukumar zabe na jihar Yobe, Dr. Muhammad Mamman, ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya a asibitin koyarwa na garin Damaturu.
Rahotannin da Daily Trust ta wallafa sun tabbatar da cewa, marigayin ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya, inda ya bar mata uku da ’ya’ya 33 da jikoki.
Wasu rahotanni daga jaridar Daily Trust sun bayyana cewa an yi jana’izarsa da safe a babban masallacin fadar Mai Martaba Sarkin Fika a Potiskum, Jihar Yobe, inda jama’a da dama suka halarta domin yi masa addu’o’i.
Dr. Mamman, wanda gogaggen likita ne ya taɓa jagorantar hukumar kula da asibitoci ta Jihar Yobe a lokacin mulkin tsohon Gwamna Ibrahim Geidam. Daga baya Gwamna Mai Mala Buni ya sake naɗa shi sau biyu a matsayin shugaban hukumar zabe ta jihar Yobe, kuma yana kan wa’adinsa na ƙarshe kafin rasuwarsa.
Marigayin ya riƙe matsayin babban likita na Masarautar Fika, daga bisani kuma aka ɗaukaka shi zuwa Shamakin Fika. Ya kasance mutum mai tawali’u, nagarta da kishin al’umma da fatan Allah Ya jikansa da rahama.



