Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce ficewar wasu gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar APC ta tabbatar da goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wike ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin kaddamar da wasu ayyuka a Abuja.
Ya ce wasu daga cikin wadannan gwamnonin sun taba zarginsa da rusa jam’iyyar PDP da kuma yi wa APC aiki, amma yanzu sun bar PDP suka koma jam’iyyar da suka dade suna zarginsa da goyon baya,inda yace ya kamata su yaba masa saboda ya yi musu hanya.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa a cikin kwanaki kalilan da suka gabata, Gwamnan Enugu, Peter Mbah, da Gwamnan Bayelsa, Douye Diri, sun bar PDP suka koma APC tare da wasu ’yan majalisar jiha, lamarin da ya rage yawan gwamnonin PDP daga 11 a zuwa 8 a yanzu.