Majalisar Dattawan Nijeriya ta shirya tantance Farfesa Joash Amupitan, wanda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zaba domin zama sabon shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC, a ranar Alhamis, 16 ga Oktoba 2025.
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da sanarwar daraktan yada labarai na majalisar, Bullah Audu Bi-Allah, ya raba wa manema labarai a Abuja a ranar Laraba.
A cikin sanarwar an bukaci kafofin yada labarai da gidajen talabijin da su watsa yadda zaman zai kasance kai tsaye domin al’umma su gani.



