Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci rundunar soji, ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro su yi hadin gwiwa tare da aiki domin dakile yawaitar hare-haren ’yan bindiga a kananan hukumomin Kebbe da Tambuwal na Jihar Sokoto.
Bukatar ta biyo bayan kudurin da dan majalisa mai wakiltar Kebbe/Tambuwal, Hon. Abdussamad Dasuki, ya gabatar a zauren majalisa ranar Talata.
Dasuki ya nuna damuwa kan yadda rashin tsaro ke ta karuwa a yankin, inda ya ce hare hare da dama da suka faru tsakanin watan Yuli da Agusta 2025,an yi garkuwa da mutane tare da halaka mutane da dama da kuma raba al’ummomi da muhallansu.
Bisa wannan dalilin majalisar ta umarci hukumomin tsaro da su kara tura jami’ai da kuma hada kai wajen gudanar da aiki a yankunan da abin ya shafa.



