Majalisar wakilan Nijeriya ta gayyaci Gwamnan babban bankin CBN, Olayemi Cardoso, tare da shugabannin manyan bankuna domin bayyana dalilin cajin kudade ba tare da daliliba daga asusun al’umma a fadin kasar.
Wannan mataki ya biyo bayan kudurin da dan majalisar mai wakiltar Ilorin West/Asa, Hon. Muktar Shagaya, ya gabatar a zaman majalisar ranar Talata, inda ya zargi bankuna da yin cajin kudade da yawa ba tare da dalili ba, wanda hakan ya saba da dokokin da CBN ta shimfiÉ—a.
Ya ce irin wannan dabi’a tana lalata amincewar jama’a ga bankuna da kuma taimakawa wajen hana jama’a rungumar ajiye kudade a bankuna.
Majalisar ta umarci kwamitin tsare-tsaren bankuna da ya gudanar da zaman bincike cikin makonni huÉ—u, tare da umartar Cardoso da shugabannin bankuna su bayyana yadda ake cire kudaden da kuma daukar mataki.