Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Sanata Samaila ya sanar da hakan ne cikin wata wasika da ya aike wa shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, wadda aka karanta a zaman majalisar na ranar Talata.
A cewar sa, rikice rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar PDP suna daga cikin manyan dalilan da yasa shi sauya shekar.
Sanatan ya bayyana cewa, ya yanke shawarar komawa jam’iyyar APC ne saboda irin sauye sauyen da shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa, masu cike da hangen nesa.