Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya zai bunkasa da kashi 3.9 cikin ɗari a shekarar 2025, wanda ya zarta hasashen da ta yi a baya da kashi 0.5 cikin ɗari.
A cewar rahoton IMF da aka gabatar a taron shekara-shekara na bankin Duniya da IMF a birnin Washington DC ranar Talata, an samu wannan hasashe ne saboda daidaituwar tattalin arziki, karuwar masu zuba jari, da kuma fitar da man fetur.
Rahoton ya nuna cewa a 2026 tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da karuwa zuwa kashi 4.2 cikin ɗari musamman yadda darajar Naira ta karu.
Bankin Duniya ma ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai samu ci gaba da kashi 4.4 cikin ɗari a 2027, wanda zai samu ne daga ɓangaren harkokin noma.