Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa har yanzu ba a saki wani daga cikin mutanen da shugaba Tinubu ya yi wa afuwa ba.
Babban lauyan gwamnati kuma Ministan shari’a, Lateef Fagbemi SAN, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Alhamis dinnan.
Ya ce duk da amincewar majalisar koli ta kasa ana cikin matakin ƙarshe na duba da tabbatar da sunayen waɗanda suka cancanci afuwa kafin fitar da takardun saki.
Fagbemi ya jaddada cewa babu wani jinkiri a cikin tsarin, illa dai gwamnati na bin doka da ka’idoji don tabbatar da gaskiya da adalci,ana bin tsarin doka ne don tabbatar da cewa duk wanda aka yi wa afuwa ya cancanta