Rundunar ‘yan sanda ta babban birnin tarayya Abuja, ta sanar da fara aikin Dantawaye Miller a matsayin kwamishina na 34 da zai jagoranci rundunar a Abuja.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar a Juma’ar nan, ta ce Miller ya karɓi ragamar ofishin daga tsohon kwamishina Ajao Adewale, wanda ya samu sabon mukami.
A cewar sanarwar, sabon kwamishinan ya yi alkawarin yin aiki tukuru tare da haɗin kai tsakanin rundunar da al’umma domin tabbatar da zaman lafiya a birnin tarayya Abuja.
Rundunar ta kuma roƙi jama’a su ci gaba da ba ‘yan sanda hadin kai wajen yakar muggan laifuka da tabbatar da tsaro.