Gwamnonin jam’iyyar APC sun gudanar da taron sirri a daren Alhamis a gidan gwamnatin jihar Kebbi, da ke Birnin Kebbi.
Rahotanni sun bayyana cewa taron ya gudana ne karkashin kungiyar gwamnonin jam’iyyar mai suna Progressive Governors Forum, wanda ta hada dukkan gwamnoni daga jam’iyyar APC a fadin Nijeriya.
Jaridar Punch ta rawaito cewa taron ya mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi siyasa da jam’iyyar da kuma yadda gwamnonin za su hada kai wajen tallafawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.