An shirya rantsar da Kwamandan soji Michael Randrianirina a matsayin shugaban kasar Madagascar bayan da sojoji suka karbe ikon kasar daga hannun shugaba Andry Rajoelina wanda ya gudu daga kasar.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa kotun kolin kasar ce za ta tabbatar da nadin Randrianirina a ranar Asabar, bayan mako guda da hambatar da gwamnatin farar hula.
Sai dai kwamandan sojin Randrianirina, wanda ke jagorantar rundunar CAPSAT, ya musanta cewa juyin mulki ne suka yi.
Rahotanni sun ce tsohon shugaban kasar, Andry Rajoelina, ya tsere ne zuwa tsibirin Reunion na Faransa, daga nan kuma aka ce ya isa Dubai.