Mazauna yankin jihar Neja ta Arewa sun gudanar da addu’o’i na musamman a filin Idi da ke Kontagora, hedkwatar karamar hukumar Kontagora, domin neman taimakon Allah kan hare-haren ’yan bindiga da ke addabar al’ummomin karkara a yankin.
Rahotanni sun bayyana cewa, yankuna kamar Magama, Mariga, Rijau, Borgu, Kontagora da Mashegu sun fuskanci hare-hare a makonnin baya-bayan nan, lamarin da ya tilasta wa mata da yara da dama barin gidajensu.
Wani daga cikin ‘yan gudun hijirar da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa, daruruwan mutane daga yankunan da ke fama da matsalar tsaro sun halarci taron addu’ar, inda suka roƙi Allah ya kawo musu saukin hare-haren ‘yan bindigar da masu basu bayanai da ma waɗanda ke tallafa musu.
Wasu mazauna yankin sun koka da cewa, sun tsere daga gidajensu yayin da ’yan bindiga suka kai farmaki a ƙauyukan nasu inda wasu suka kwana a kan duwatsu, wasu kuma suka koma Kontagora don tsira da rayukansu.