Bayanai daga kauyen Tittike da ke mazabar Boko a karamar hukumar hukumar Kusada jihar Katsina na cewa barayin daji sun kai hari inda suka yi sanadiyyar asarar dumbin dukiyoyi.
A cikin wani sakon jajanta wa da dan majalisar wakilai daga kananan hukumomin Kankia/Kusada/Ingawa Abubakar Yahaya Kusada ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya jajanta bisa wannan abin da ya kira ibtila’i.
Ya ce “Cikin alhini da kaduwa nake mika sakon jajantawa ga Al’ummar TITTIKE dake Boko ward, a karamar hukumar kusada bisa ibtila’in shigowar yan bindiga”.
“Al’ummarmu sun yi asarar dukiyoyinsu da kuma daukar daya daga cikin matasanmu da muke alfahari da shi wato Malam Kamilu Abdurrahman Tela. Ina jajanta mana bisa wannan ibtila’i da ya shafi Al’ummarmu”.
Ba za mu gajiya ba wajen shige da fice da muke yi don ganin wannan matsala ta zama tarihi, Allah ya ba mu mafita Amin”.
Karamar hukumar Kusada dai na iyaka da Kankia, inda ake samun matsalar tsaro jefi-jefi a jihar Katsina