Akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu bayan hatsaniya ya barke tsakanin wasu da ake zargin ’yan bindiga da masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a kauyen Kuyello da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, a ranar Alhamis.
Lamarin da ya faru da misalin ƙarfe 11 na safe ya jefa al’ummar yankin cikin tashin hankali, inda aka ji karar harbe-harbe da suka tilasta mazauna yankin tserewa cikin daji domin tsira da rayukansu.
Rahotannin jaridar Punch sun bayyana cewa rikicin ya faru ne bayan wani da ake zargin dan bindiga ya nemi haraji daga masu hakar ma’adanai, amma suka ƙi biya, lamarin da ya haifar da saɓani har ta kai ga kashe shi.
Bayan faruwar hakan, wasu daga cikin abokan aikinsa suka dawo tsakiyar rana suna harbin kan-mai-uwa-da-wabi, inda suka kashe mutane da dama ciki har da wasu daga cikin masu hakar ma’adinai.



