Kungiyar kare haƙƙin jama’a da tabbatar da shugabanci na gaskiya a Nijeriya SERAP ta nemi shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas, su bayyana yadda aka kashe naira biliyan 18.6 da aka biya don gina ofishin hukumar kula da ayyukan majalisar kasar.
SERAP ta kuma bukaci su bayyana sunan kamfanin da ya karɓi kuɗin tare da sunayen jagororinsa da adireshinsa.
Kungiyar ta ce akwai zargin karya dokar bayar da kwangila ta Nijeriya da rashin takardar amincewa daga hukumar BPP ko majalisar zartarwa ta tarayya.
A cewar sanarwar da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ya fitar, kungiyar ta ce bayyana gaskiya kan lamarin zai tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa majalisar tana aiki don amfanin jama’a ba don wasu keɓantattu ba.
Rahoton mai binciken asusun gwamnati na shekarar 2022 wanda jaridar Punch ta wallafa ya nuna cewa hukumar ta biya naira biliyan 11.6 ga wani kamfani da ba a bayyana sunansa ba domin gina sabon gini cikin watanni 24, kafin daga baya a ƙara Naira biliyan 6.9 ba tare da takardar izini ko amincewa daga hukuma ba.