Sakataren jam’iyyar ADC Ogbeni Rauf Aregbesola, ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da rashin jurewa ra’ayoyin ‘yan adawa da kuma amfani da ƙarfin gwamnati wajen murkushe su .
Aregbesola ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da ofishin ADC a garin Ilori jihar Kwara, inda ya ce gwamnatin APC ta gaza saboda son kai da rashin ƙwarewa, abin da ya jefa ƙasar cikin yunwa, rashin tsaro da durkushewar ayyukan gwamnati.
Ya kara da cewa yanzu haka yunwa ta mamaye ƙasa, ta mayar da mulki hanyar tara wa kai dukiya da tsoratar da ‘yan adawa.
Aregbesija ya ce ‘yan Nijeriya na fama da wahala saboda gazawar shugabanni a karkashin APC.
Hakazalika, jaridar Punch ta ruwaito Aregbesola ya ce, jam’iyyar ADC ita ce jam’iyyar da ke da muradin gaskiya da hidima ga jama’a, sannan abin dogaro ga ‘yan Nijeriya gabanin zaben 2027.
A cewarsa, ƙiyayyar ‘yan Nijeriya ga APC ta bayyana, kuma ADC ce za ta amfana da hakan.



