Jam’iyyar hadaka ta ADC reshen jihar Adamawa ta bayyana tsohon shugaban Nijeriya Atiku Abubakar da tsohon sakataren gwamnatin ƙasar Babachir Lawal a matsayin mambobin bogi.
Shugaban jam’iyyar ADC a Adamawa Shehu Yohanna, shi ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da jaridar Punch, inda ya ce ‘yan siyasar za su fita daga wannan layin ne da zarar sun yanki katin zama cikakkun mambobi.
Kafin wannan lokaci dai, Atiku Abubakar ya nuna goyon bayansa ga tafiyar ADC bayan ficewa daga PDP, sai dai ya jinkirta tabbatar da kansa a matsayin dan jam’iyyar a hukumance.