Gwamnatocin Kenya da Senegal sun bai wa juna damar shige da fice ga ‘yan kasashensu ba tare da biza ba na tsawon kwanaki 90.
DW Africa ta ruwaito cewa daukar matakin kulla yarjejeniyar ya biyo bayan ziyarar da shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya kai kasar ta Kenya, inda ya gana da shugaba William Ruto.
Kazalika bangarorin biyu sun sha alwashin kyautata alaka da kuma inganta harkokin kasuwanci a tsakanin su.