Majalisar dattawan Nijeriya ta bukaci gwamnati ta sake yin duba kan albashin da ake biyan jami’an tsaro musamman ma soji a fadin kasar.
Majalisar ta bayyana cewa dalilin wannan kira shi ne ta damu matuka da yadda ake fama matsin tattalin arziki baya ga tsadar rayuwa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kiran ya biyo bayan kudirin da Sanata mai wakiltar Borno ta kudu kuma tsohon bulaliyar majalisar Ali Ndume ya gabatar a zamanta na yau Talata.
A cewar Ndume, duba da yadda jami’an tsaron Nijeriya ke sadaukar da rayukansu wajen kare ‘yan kasa, akwai bukatar a inganta albashi har ma da walwalar su.
Ya kuma kara da yin tuni ga majalisar cewa sojoji a wasu kasashen Afirka da dama na samun albashi fiye da na Nijeriya.