Gwamnan jihar Nassarawa Abdullahi Sule ya ce guguwar sauyin sheka tsakanin ‘yan siyasa da ake samu a baya bayan nan musamman ga masu shiga APC, na da alaka kai tsaye da manufofin shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu.
Yayin da yake jawabi a wajen bikin sake karbar Sanata Ahmed Wadada mai wakiltar Nassarawa ta yamma cikin jam’iyyar APC a birnin Lafia, gwamna Sule ya ce babban burin shugaba Tinubu shi ne ciyar da Nijeriya gaba ta kowace fuska.
Jaridar Punch ta ruwaito gwamnan na yabawa Sanata Wadada da magoya bayansa, yana mai cewa sun dauki matakin da ya dace, na barin jam’iyyar SDP.