Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bayyana shirin bayar da aron matashin dan wasanta na gaba Endrick.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa tuni Real Madrid ta fara tattaunawa da kungiyoyi da dama masu sha’awar daukar dan wasan, wanda zai bar kungiyar a kasuwar cinikayyar ‘yan wasa ta watan Janairu.
Tun a shekarar 2022 Real Madrid ta sayi dan wasan na kasar Brazil, sai dai yana fuskantar kalubale na rashin isasshen lokacin fafata wasanni a kungiyar, daidai lokacin da ake tunkarar gasar cin kofin duniya na shekarar 2026.