Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunan Dr. Bernard Mohammed Doro daga jihar Filato ga majalisar dattawa don nada shi minista a gwamnatinsa.
Bayanin aike wa da sunan na sa na kunshe cikin sanarwa da fadar gwamnatin Tinubu ta fitar.
Dr. Bernard Mohammed Doro dai ya kasance kwararre a bangaren lafiya, inda ya samu gogewa ta tsawon shekaru yana aiki a fannin a ciki da wajen Nijeriya.
Wannan ya zo ne bayan da aka zabi Farfesa Nentawe Yilwatda daga jihar ta Filato a matsayin shugaban jam’iyyar APC na Nijeriya.



