Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya gode wa al’ummar jihar bisa irin tarbar da suka yi wa mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima, yayin ziyarar kwanaki biyu da ya kai jihar.
Radda ya ce wannan goyon baya da jama’a suka nuna ba sabon abu ba ne, domin tun farkon tafiyarsa a siyasa suna tare da shi, lamarin da ke kara masa kwarin guiwar gudanar da ingantaccen mulki.
Gwamnan ya kuma ce duk nasarorin da gwamnatinsa ke samu, baiwa ce daga Allah tare da goyon bayan tawagarsa da kuma amincewar jama’ar jihar.
Ya kara da cewa hakan shi ne ginshikin sauye-sauyen da ake gani a fadin jihar Katsina.