Kafar yaɗa labarai ta DCL Hausa ta sanar da buɗewar damar neman aiki ga masu ƙwarewa a fannin gyaran bidiyo (Video Editing) domin cike gurbin ma’aikaci a ofishinta na jihar Katsina.
A cikin sanarwar da ta fitar, DCL Hausa ta bayyana cewa ana buƙatar mai kwarewa a aikin gyaran bidiyo wanda zai taimaka wajen gyara rahotanni, labarai, da bidiyoyin sada zumunta, tare da tabbatar da ingancin hoto da sauti.
DCL Hausa ta buɗe ƙofa ga mai kwarewa a aikin gyaran bidiyo wanda ke da hangen nesa, da sha’awar samar da ingantaccen bidiyo ga masu kallonmu.
Abubuwan da ake bukata (Requirements):
- Mazauni jihar Katsina.
- Mai Ƙwarewa wajen gyaran bidiyo.
- Iya amfani da Adobe Premiere Pro da Canva – kwarewa da sauran software irin su CapCut ƙarin fa’ida ne.
- Kwarewa wajen haɗa rahotanni, labarai, da bidiyoyin sada zumunta.
- Fahimtar dabarun haɗa sauti da hoto don samar da ingantaccen bidiyo.
- Iya aiki cikin lokaci da bin tsarin aiki da aka gindaya.
- Sha’awar kirkira da fasaha a fagen yada labarai.
- Ƙwarewa wajen aiki tare da sauran ma’aikata (teamwork) da kyakkyawar mu’amala.
- Mata za su iya neman wannan gurbin!
Cike bayananka/ki nan: https://forms.gle/EJnCwJhdM2nHY8vs9
Ana sa ran wanda ya yi nasara zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Nuwamba, 2025.
Za a kulle kofa karɓar bayanai a ranar Lahadi, 26 ga Oktoba, 2025.