Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Nijeriya FRSC ta bayyana cewa a mafiya yawan lokuta rashin hakuri, gudun wuce sa’a tare da karya dokokin hanya ne ke haifar da hadura a titunan kasar.
Kwamandan hukumar na yankin Okitipupa a jihar Ondo shi ne ya bayyana haka, yayin wani taron wayar da kai game da zirga-zirgar ababen hawa a lokacin bukukuwan karshen shekara.
Hukumar ta kuma nuna damuwa da cewa an fi samun ire-iren wadannan hadurra a watannin karshen shekara da ake samun bukukuwa a cikin su, kamar yadda The Nation ta ruwaito.



