Jam’iyyar hadaka ta ADC mai hamayya a Nijeriya reshen Kaduna ta kori mataimakin shugabanta na jihar tare da wasu manyan jami’anta guda takwas, bayan samun su da aikata laifukan da suka saba wa dokokinta.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa yayin wani taron manema labarai a Kaduna, shugaban jam’iyyar na jihar Elder Patrick Ambut, ya ce korar mutanen ya zama wajibi ne kasancewar ba za ta lamunci duk abin da zai kawo hargitsi ko zubar mata da kima ba.
Jam’iyyar ta zargi wadanda ta kora da aikata laifukan gudanar ta tarukan sirri don shirya manakisa kan shugabanci, tatsar kudi daga mambobin jam’iyyar, da kuma sabawa ka’idoji.