DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tsohon Minista Tanimu Turaki ya zama ɗan takarar shugabancin jam’iyyar PDP na Arewa

-

Jagororin jam’iyyar PDP na yankin Arewacin Nijeriya sun amince da tsohon Ministan Harkoki. A Musamman, Tanimu Turaki (SAN), a matsayin ɗan takarar da suka amince domin ya yi takarar kujerar shugabancin jam’iyyar PDP na ƙasa, gabanin babban taron jam’iyyar da za a gudanar a watan Nuwamba a Ibadan, Jihar Oyo.

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, shi ne ya sanar da hakan bayan taron shugabannin PDP na Arewa da aka gudanar a Abuja daren Laraba, inda ya bayyana cewa Turaki ne ɗan takarar da aka cimma matsaya a kansa.

Ya kuma ce duk wanda bai gamsu da wannan matsaya ba, yana da ‘yancin tsayawa takara.

Jaridar Punch ta ruwaito a baya cewa tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Makarfi,  tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido da kuma Tanimu Turaki, sune kan gaba wajen neman wannan kujera, wacce za a yanke hukunci kanta a taron masu ruwa da tsaki na yankin a wannan makon.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Jam’iyyar ADC a Kaduna ta kori mataimakin shugabanta da wasu ‘ya’yanta 8

Jam'iyyar hadaka ta ADC mai hamayya a Nijeriya reshen Kaduna ta kori mataimakin shugabanta na jihar tare da wasu manyan jami'anta guda takwas, bayan samun...

Hukumar FRSC ta bayyana dalilan yawan afkuwar hadura a titunan Nijeriya

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Nijeriya FRSC ta bayyana cewa a mafiya yawan lokuta rashin hakuri, gudun wuce sa'a tare da karya dokokin hanya ne...

Mafi Shahara