Jagororin jam’iyyar PDP na yankin Arewacin Nijeriya sun amince da tsohon Ministan Harkoki. A Musamman, Tanimu Turaki (SAN), a matsayin ɗan takarar da suka amince domin ya yi takarar kujerar shugabancin jam’iyyar PDP na ƙasa, gabanin babban taron jam’iyyar da za a gudanar a watan Nuwamba a Ibadan, Jihar Oyo.
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, shi ne ya sanar da hakan bayan taron shugabannin PDP na Arewa da aka gudanar a Abuja daren Laraba, inda ya bayyana cewa Turaki ne ɗan takarar da aka cimma matsaya a kansa.
Ya kuma ce duk wanda bai gamsu da wannan matsaya ba, yana da ‘yancin tsayawa takara.
Jaridar Punch ta ruwaito a baya cewa tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Makarfi, tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido da kuma Tanimu Turaki, sune kan gaba wajen neman wannan kujera, wacce za a yanke hukunci kanta a taron masu ruwa da tsaki na yankin a wannan makon.