Jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya karyata zargin da ake yi masa na tsoma baki a harkokin mulkin Jihar Kano ko raba kwangiloli.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC Hausa, inda ya ce waɗannan zarge-zargen ba su da tushe, kuma ba ya ganin buƙatar ya mayar da martani ga masu adawa da shi.
Madugun darikar Kwankwasiyyar ya kara da cewa, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf shi ne ke tafiyar da mulkinsa gaba ɗaya, kuma shi ne aka zaɓa da cikakken nazari tun bayan zaɓen 2019 kuma yanzu yana aiki cikin gaskiya da natsuwa, mu kuma mun ba shi dama ya yi aikinsa.
Tsohon gwamnan ya kuma musanta zancen cewa akwai rikici a jam’iyyar NNPP, yana mai cewa masu yada irin wannan magana ba ‘yan siyasa na gaskiya ba ne kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.