DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Kamaru ta takaita amfani da intanet yayin da ake zaman dar-dar game da sakamakon zaben shugaban kasa

-

Gwamnatin ƙasar Kamaru ta takaita amfani da intanet a wasu sassa na ƙasar a ranar Alhamis, yayin da ake zaman dar-dar saboda jinkirin bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar ranar 12 ga watan Oktoba, 2025.

Rahotanni sun nuna cewa biranen Yaoundé, Douala, Buea, Garoua, Maroua da Bamenda suna fuskantar cikas wajen amfani da manhajojin sada zumunta da sakonni, inda ma wasu ke cewa VPN ma ba ya aiki. Ana ganin wannan wata alama ce ta matakin gwamnati na takaita intanet na ɗan wani lokaci.

Google search engine

Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce daga kungiyoyin farar hula da ‘yan adawa, wadanda ke zargin gwamnati da yunkurin boye bayanai da sarrafa sakamakon zaɓen.

Madugun adawa kuma dan takarar shugaban ƙasa, Issa Tchiroma Bakary, ya ce akwai alamun murɗa sakamako, yayin da kungiyoyin sa-ido kan dimokuraɗiyya suka ce matakin zai rage yarda da tsarin mulki.

Masu nazari sun gargadi cewa takaita intanet a irin wannan lokaci na siyasa mai cike da rashin tabbas na iya ƙara haifar da rikice-rikice da rashin kwanciyar hankali a tsakanin magoya baya, kamar yadda jaridar Mimi Mefo Info ta ruwaito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Hukumar Tarayyar Turai ta yi Allah-wadai da haramta biza da Amurka ta yi wa wasu Turawa

Tarayyar Turai, tare da ƙasashen Faransa da Jamus, sun yi kakkausar suka ga matakin Amurka na haramta biza ga wasu ’yan Turai da ke yaki...

Shugaba Tinubu ya yi kira ga hadin kai da hakuri a tsakanin addinai a cikin sakon taya murnar bikin Kirsimeti

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su rungumi haɗin kai, juriya da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, yana mai cewa...

Mafi Shahara