Majalisar Wakilan Nijeriya ta amince da gudanar da bincike kan rancen dala miliyan 460 da gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta karɓa daga kasar China domin saka na’urorin CCTV an Abuja.
Wannan na zuwa ne bayan kudiri na gaggawa da dan majalisa Amobi Ogah, mai wakiltar mazabar Isuikwuato/Umunneochi ta jihar Abia ya gabatar a zaman majalisar na ranar Laraba.
Dan majalisar ya bayyana cewa an karɓi bashin ne tun shekarar 2010 domin sanya na’urorin tsaro a manyan wurare na Abuja, amma har yanzu aikin bai kammalu ba duk da cewa ana biyan bashin rancen.
Ogah ya kara da cewa, lamarin na da muhimmanci a sake dubawa ganin yadda matsalar tsaro ke ƙaruwa a birnin Abuja.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, a baya, majalisar ta 9 ta 2019 ta tambayi ma’aikatar kudi kan matsayin aikin, inda tsohuwar ministar kudi Zainab Ahmed ta tabbatar ana biyan bashin amma ba ta bayyana yadda aka kashe kuɗin ba.
Hakazalika, binciken zai taimaka wajen gano inda kudaden suka tafi da kuma dalilin da yasa aikin bai aiwatu ba duk da rancen da aka karɓa shekaru fiye da 10.



