Jiga-jigan jam’iyyar PDP 15 daga jihar Zamfara, ciki har da shugabanni na jiha da na yankuna, sun fice daga jam’iyyar zuwa APC yayin da ake shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
An karɓe su a hukumance a birnin Abuja ta hannun Alhaji Tijjani Yahaya, wanda ya wakilci tsohon gwamnan jihar kuma sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Abdul’aziz Yari.
Cikin wadanda suka koma jam’iyyar APC akwai shugaban matasan PDP Sahad Dabo, tsohon ma’ajin jam’iyya Nasiru Anka, tsoffin sakatarorin shirya taruka Janaidu Magaji Kiyawa da Musa Halilu Faru, da Hajiya Rabi Bakura.
Alhaji Tijjani Yahaya ya bayyana cewa Yari tare da ministan tsaron, Bello Matawalle, za su shirya biki na musamman domin tarbar sabbin ‘yan jam’iyyar idan sun dawo ƙasa. Sannan kuma, sabbi da tsofaffin mambobin za su ci moriyar jam’iyyar ba tare da nuna bambanci ba.
A nasa bangaren, shugaban APC na jihar Zamfara, Tukur Umar Danfulani, ya yaba da ƙoƙarin Yari da Matawalle wajen ƙarfafa jam’iyyar a fadin jihar.



