Wani matashi mai shekaru 25 da haihuwa mai suna Hammed Tunde, ya rasa ransa bayan abokinsa mai suna Gafar ya yi ajalin abokinsa da wuka a kirji sakamakon gardama da suka yi kan wata budurwa a unguwar Oja Gboro, cikin birnin Ilori, jihar Kwara.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata yayin da su biyun ke sayen rake a wajen wani mai sayarwa inda wani shaidu suka ce gardamar da ta fara da barkwanci ta rikide zuwa fada, inda Gafar, wanda ke da shekaru 21, ya fitar da wuka ya yi ajalin abokinsa.
Marigayin wanda ke zaune a Ile-Soro 2, Oja Gboro, an garzaya da shi zuwa wani asibiti mai zaman kansa, amma daga bisani aka tura shi asibitin gwamnati na Ilorin, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
Gafar kuma, wanda asalin dan Ile Olowo ne a yankin, ya tsere daga wajen bayan aikata laifin, kuma har yanzu ba a same shi ko ‘yan uwansa ba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa kwamishinan ‘yan sanda, CP Adekimi Ojo, ya umurci da gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da an cafke wanda ake zargi.



