DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ƴan Nijeriya sun rage fita kasashen waje neman lafiya karkashin mulkin Tinubu – Rahoton jaridar Punch

-

Babban bankin Nijeriya, CBN ya bayyana cewa ’yan Nijeriya sun kashe dala miliyan 4.74 wajen neman lafiya a kasashen waje daga Mayu 2023 zuwa Maris 2025, watanni 22 na farko a mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Rahoton da jaridar Punch ta wallafa ya nuna cewa, adadin ya ragu da kashi 52 cikin 100 idan aka kwatanta da dala miliyan 9.83 da aka kashe a lokacin watanni 22 na farkon mulkin tsohon shugaba Muhammadu Buhari. Wannan raguwar na iya zama sakamakon tsauraran dokokin musayar kudade da kuma karuwar neman lafiya a cikin gida.

Google search engine

Kididdigar ta nuna cewa, daga Mayu zuwa Disamba 2023, an kashe dala miliyan 2.28, yayin da a 2024 aka kashe dala miliyan 2.40. A farkon 2025 kuwa, an kashe dala 0.06 kacal, babu kuma wani kudi da aka fitar a watan Fabrairu da Maris, 2025

A zamanin Buhari, daga Mayu 2015 zuwa Fabrairu 2017, ’yan Nijeriya sun kashe dala miliyan 9.83 wajen jinya a kasashen waje, adadin da ya nuna cewa, amfani da kudin neman lafiya a waje ya ragu sosai a lokacin shugaba Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsare-tsaren Tinubu na farfaɗo da martabar Nijeriya a duniya -Kashim Shatima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa na sake gina martabar Nijeriya a idon duniya tare...

Gwamnatin Nijeriya na shirin dakatar da shigo da kayan tsaro daga waje

Gwamnatin Nijeriya ta yi niyyar kera dukkan makami da ake buƙata a cikin gida nan da shekara biyu zuwa biyar masu zuwa. Minista a ma'aikatar Tsaron...

Mafi Shahara