Majalisar Tattalin Arzikin Nijeriya ta bayyana cewa za ta fara wani gagarumin samame kan masu hakar zinare da sauran ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba domin kare albarkatun ƙasa da kuma ƙara yawan kudaden shiga na gwamnati.
Wannan mataki ya biyo bayan shawarar fadada aikin kwamitin da NEC ta kafa kan hana satar man fetur, ƙarƙashin jagorancin gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, domin ya haɗa da yaki da hakar ma’adinai da kuma safarar su ta ɓoye.
Da yake wa manema labarai bayani bayan zaman NEC karo na 153 a fadar shugaban Nijeriya, Uzodinma ya ce sabon alhakin kwamitin zai taimaka wajen toshe barakar asarar kuɗin shiga daga ma’adinan ƙasa, haka kuma an gabatar da rahoton wucin-gadi ga majalisar kuma an karɓe shi da farin ciki, tare da faɗaɗa aikinmu domin kula da ma’adinai kamar zinare da ake sacewa ba tare da ƙasar na cin gajiyarsu ba.
Uzodinma ya kara da cewa, kwamitin zai yi aiki tare da ma’aikatar ma’adinai, hukumomin da abin ya shafa da na tsaro domin dakile safarar zinare da hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.



