Majalisar wakilan Nijeriya ta karanta kudirin doka karo na biyu da ke neman gyara dokar kafa EFCC ta 2004 domin ba wa hukumar cikakken ‘yancin aiki ba tare da tsoma bakin siyasa ba.
Kudirin da ɗan majalisa daga jihar Filato, Yusuf Gagdi ya gabatar, ya ce gyaran zai sabunta tsarin hukumar da ya tsufa tun 2004.
Gagdi ya bayyana cewa laifukan kudi sun ƙaru da sababbin dabaru kamar safarar kudi ta yanar gizo da amfani da kudaden kirifto, sannan kuma dokar ba ta ba da kariya daga tsoma bakin siyasa.
Sabon kudirin na neman a rage ikon shugaban ƙasa wajen sauke shugaban EFCC, inda dole ne a samu amincewar kaso biyu bisa uku na majalisa kafin cire shi.
Gagdi ya kara da cewa, wannan gyaran zai tabbatar da sahihanci da ‘yancin hukumar, ƙarfafa amincewar jama’a, da karfafa yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya.



