Hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta bayyana karbar ‘yan kasar 150 da suka makale a kasar Nijar.
Bayanin na kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, inda ta ce ‘yan Nijeriyar sun sauka a filin jirgin sama na Aminu Kano, da ke jihar Kano.
Labari mai alaka:Â Hukumar NEMA ta karbi ‘yan Nijeriya 147 da suka makale a Libya
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan mataki yana cikin shirin mayar da mutane ainahin kasashensu, hadin gwiwa da gwamnati tare da majalisar dinkin duniya.
Hukumar NEMA ta ce cikin wadanda aka dawo da su akwai maza 88 da mata 32, sai kuma yara maza 14 da yara mata 16.



