Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai manyan jami’an sojin Nijeriya masu mukamin Janar akalla 60 da za su fuskanci ritayar dole, biyo bayan sauye-sauyen da shugaba Tinubu ya yi a fannin tsaron kasar.
Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda lamarin zai shafa sun kasance a saman sabbin hafsoshin da aka nada a girman matsayin aiki.
Majiyoyi sun shaidawa jaridar cewa hakan wani mataki ne na tabbatar da bin ka’idojin aikin soji.
Shugaba Tinubu dai ya sauya manyan hafsoshin tsaron Nijeriya ne tare da maye gurbinsu da wasu, lamarin da gwamnati ta bayyana a matsayin wani mataki na karfafa tsaron kasar.
Labari mai alaka: Ka fito ka bayyana wa ‘yan Nijeriya hakikanin dalilin da ya sa ka canza hafsoshin tsaro – Bukatar ADC ga shugaba Tinubu



