Tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ya ki tsayar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Elrufa’i don ya gaje a shekarar 2007 ne saboda rashin gogewar sa a siyasa.
Labari mai alaka: Jonathan ne dantakara mafi nagartar da zai tsaya wa PDP takara a zaben 2027 – Sule Lamido
Obasanjo ya bayyana haka ne Abeokuta, jihar Ogun, inda ya ce a wancan lokacin, tsohon ministan sufurin jiragen sama na Nijeriya Osita Chidoka ya ba shi shawarar daukar El-Rufai, sai dai ya mayar da martanin cewa akwai bukatar ya kara samun gogewa.
Obasanjo dai ya tsayar da marigayi Umaru Musa ‘Yar Aduwa a matsayin wanda zai gaje shi bayan sauka daga shugabancin Nijeriya, a shekarar 2007.



