DCL Hausa Radio
Kaitsaye

ADC ta dakatar da Dr. Sule-Iko daga jam’iyyar a jihar Kebbi

-

Jam’iyyar ADC reshen jihar Kebbi ta sanar da dakatar da Dr. Sule-Iko Sadeeq S. Sami daga jam’iyyar nan take, saboda abin da ta kira ya nada kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na jiha ba bisa ka’ida ba.

A cewar sanarwar da sakataren yada labaran jam’iyyar ADC a jihar Kebbi, Engr Abubakar Atiku Musa ya fitar, jam’iyyar ta dauki matakin ne bayan babban kwamitin jam’iyyar na kasa NWC ya tabbatar da cewa dukkan shugabannin jihohi na riko za su ci gaba da rike mukamansu har zuwa karshen wa’adinsu a watan Mayu 2026.

Google search engine

Sanarwar ta ce babban kwamitin jam’iyyar na jiha SWC ya yanke shawarar dakatar da Dr. Sule-Iko daga jam’iyyar tare da gargadinsa da kada ya sake shiga ko halartar wani taron jam’iyyar. Haka kuma ta tabbatar da cewa Engr Sufiyanu Bala shi ne shugaban jam’iyyar ADC na jihar Kebbi da doka ta amince da shi.

Jam’iyyar ta bukaci hukumomin tsaro da su dauki mataki domin hana Dr. Sule-Iko ci gaba da gudanar da ayyuka ko magana da sunan jam’iyyar, tare da kira ga mambobi da jama’a su yi watsi da duk wata sanarwa daga gare shi da ba ta fito daga shugabancin da hukuma ta amince da shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu kai ƙarar APC gaban ECOWAS kan musguna wa mambobinmu – Jam’iyyar ADC

Jam’iyyar haɗaka ta ADC ta ce za ta kai ƙorafi gaban Ƙungiyar ci-gaban kasashen yammacin Afrika ECOWAS da sauran ƙasashen duniya kan hare-haren da ake...

Manyan Jami’an soji za su fuskanci ritayar dole bayan sauye-sauye a fannin tsaron Nijeriya

Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai manyan jami'an sojin Nijeriya  masu mukamin Janar akalla 60 da za su fuskanci ritayar dole, biyo bayan sauye-sauyen da...

Mafi Shahara