Kungiyar Juventus ta sallami kocinta Igor Tudor a ranar Litinin bayan shan kashi da ci 1-0 a hannun Lazio, wanda ya sa kungiyar ta tara maki biyar kacal a wasanni biyar da suka gabata.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito kungiyar ta sanar da cewa Massimiliano Brambilla zai jagoranci tawagar a wasan da za su fafata da Udinese ranar Laraba.
A cikin sanarwar, Juventus ta gode wa Tudor da tawagarsa bisa jajircewa da ƙwarewar da suka nuna tun lokacin da ya karɓi ragamar horaswar a watan Maris.
Juventus tana matsayi na takwas a gasar Serie A, maki shida a bayan Napoli, kuma ba ta lashe wasa ba tun ranar 10 ga Satumba ba, tana da jerin wasanni takwas ba tare da nasara ba.
Jimillar aikinsa a kungiyar, Tudor a Juventus ta kasance nasarori 10, canje 8, da rashin nasara 6, duk da kashe euro miliyan 130 wajen siyan sababbin ‘yan wasa a lokacin bazara.
Tudor, tsohon ɗan wasan tsakiyar ƙasar Croatia mai shekaru 47, ya taba buga wa Juventus wasa a lokacin da yake taka leda, kafin daga baya ya karɓi aikin horaswa daga hannun Thiago Motta a watan Maris.



