Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da shirin ƙara yawan samar da man da take tacewa daga ganga 650,000 zuwa ganga miliyan 1.4 a kowace rana, wanda idan an kammala zai zama mafi girma a duniya, ya zarce Jamnagar Refinery da ke Indiya.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai a Legas a ranar Lahadi, inda ya ce wannan mataki yana nuna aminci ga makomar Najeriya tare da daidaita da manufar Shugaba Bola Tinubu ta ganin kasar ta zama kan gaba a samar da man da aka tace a duniya.
Ya bayyana cewa wadannan manufofi sun sake fasalin sashen man fetur a ƙasa tare da karfafa zuba jari daga kamfanoni a harkar tace mai.



