DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mun raba Naira biliyan 116.4 ga ɗalibai sama da dubu 624 – Asusun NELFUND

-

Asusun ba da bashin karatu ga ɗaliban manyan makarantu ya bayyana cewa ya raba Naira biliyan 116.4 ga ɗalibai sama da dubu 624, tun bayan ƙaddamar da tsarin neman bashin a watan Mayu, 2024.

Kamar yadda rahoton da Asusun ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, 28 ga Oktoba, 2025, ya nuna, an karɓi buƙatu fiye da 929,000, inda ɗalibai 624,535 suka amfana, yayin da aka samu ƙarin sabbin masu neman bashi 12,398 a rahoton baya-bayan nan.

Google search engine

Asusun ya bayyana cewa an biya makarantu 239 Naira biliyan 65.3 a matsayin kuɗin karatu, yayin da Naira biliyan 51.1 ta shiga hannun Ɗalibai domin ciyarwa da sauran bukatun yau da kullum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Muna karɓar saƙonnin barazanar kawo mana hari a majalisa – Shugaban kwamitin tsaron majalisar waƙilai

Shugaban kwamitin tsaron cikin gida na Majalisar Wakilai, Honarabul Garba Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa majalisar na shan barazanar kai mata hari daga ’yan ta’adda,...

Sama da mutum 170 ne ke son zama ’yan Nijeriya daga kasashen ketare – Ministan cikin gida

Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji Ojo, ya bayyana cewa sama da ’yan kasashen ketare 170 ne suke neman zama ’yan Nijeriya. Tunji Ojo ya sanar da...

Mafi Shahara