Tsohon kwamishinan ilimi na a zamanin Ganduje, Muhammad Sanusi Sa’id Kiru, ya soki matakin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na mayar da Makarantar Sakandare ta ‘Yan Mata GGSS Maikwatashi zuwa Kaura Goje, yana mai cewa an yi hakan ne cikin son rai.
A wata wasika da ya rubuta wa Gwamnan, tsohon kwamishinan ya bayyana cewa, duk da yana goyon bayan kudirin gwamnatin na inganta harkar ilimi, yadda aka gudanar da wannan aiki ya nuna rashin kwarewa da kuma rashin tsari daga masu ruwa da tsaki.
Ya ce rusa tsohuwar makarantar kafin a kammala sabuwar ya haifar da matsaloli ga dalibai da malamai da mazauna yankin.
Kiru ya kuma soki abin da ya kira da sayar da filin makarantar Maikwatashi a kan Naira miliyan 100 kowace gona, yana mai cewa wannan mataki ba daidai ba ne kuma ya saba da walwalar al’umma.
A cewarsa, filin ya kamata a mayar da shi wajen gudanar da ayyukan al’umma kamar filin motsa jiki, dakin taro ko cibiyar koyar da sana’o’i.



