Dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Maradun II ta jihar Zamfara, Hon. Maharazu Salisu, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC tare da wasu manyan ‘yan jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar ta APC a jihar Tukur Danfulani ne ya karbesu a yayin taron da ya gudana a ofishin jam’iyyar APC na jihar da ke Gusau.
Hon. Salisu ya ce rashin adalci da nuna banbanci a cikin jam’iyyar PDP ne ya sa ya fice daga cikinta, inda ya bayyana cewa mazabarsa ba ta samu kulawa ko wakilci daga gwamnati bayan zaben 2023,wadannan dalilan suka sa shi sauya sheka zuwa APC.



