Shugaban kwamitin tsaron cikin gida na Majalisar Wakilai, Honarabul Garba Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa majalisar na shan barazanar kai mata hari daga ’yan ta’adda, abin da ya haifar da bukatar karfafa tsaro a cikin ginin majalisar.
Honarabul Muhammad ya bayyana hakan ne a yayin jin ra’ayi kan kudirin kafa hukumar tsaron majalisa da aka gudanar a Abuja, inda ya ce majalisar ta zama abin bibiya ga miyagu da ke amfani da raunanan matakan tsaro.
A cewarsa sun sha barazana daga ’yan ta’adda da ke cewa zasu tarwatsa ginin majalisar, haka kuma wasu masu zanga-zanga sun yi barazanar rufe ta.
Ya ce kudirin yana nufin samar da tsaron da ya dace da abin da ake amfani da shi a majalisun kasashe masu ci gaba, domin kare ’yan majalisa, ma’aikata, da duk masu ziyartar ginin.



