Matatar man Dangote ta tabbatar da cewa za ta samar da isasshen man fetur da dizal a fadin Nijeriya a lokacin bukukuwan karshen shekara domin a cewar kamfanin, yawan man da ake tacewa a kullum yanzu ya haura abin da ake bukata.
Mai kula da harkokin yada labarai da dabarun kasuwanci na rukunin kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka samu daga ofishinsa a ranar Asabar, inda ya ce matatar tana fitar da lita miliyan 45 na fetur da lita miliyan 25 na dizal a kullum.
Chiejina, ya ce kamfanin na aiki tare da hukumomi da masu rarraba man domin tabbatar da isar sa cikin sauki a fadin kasar.
A cewarsa, karuwar tace man a cikin gida na taimakawa wajen karfafa Naira ta hanyar rage kudaden da ake fitarwa waje da kuma karfafa kudaden da ke shigowa cikin gida.



